Dubun wasu masu Luwadi a jihar Sakkwato ta cika, sun fuskanci hukuncin Kotu
An kama wani dan Achaba mai suna Malami Abdullahi mai shekaru 27, dan asalin garin Kasarawa tare da wani karamin Yaro da laifin aikata Luwadi a jihar sakkwato, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito rundunar Yansandan jihar ta gurfanar da mutanen biyu gaban wata Kotun majistri dake garin Sakkwato, inda ake tuhumarsu da saba ma halittar dan Adam.
KU KARANTA: Kallabi tsakanin rawwuna: Wata daliba daga jihar Katsina ta ciri ruta a jami’ar Saudiyya
Dansanda mai shigar da kara, Sufeta Abubakar Tambuwal ya bayyana ma Kotun cewa an kama mutanen biyu ne a ranar 7 ga watan Mayu, a lokacin da suke tsaka a aikata laifin da ake tuhumarsu akai, ya kara da cewa sau uku ana kama su suna Luwadin a kan hanyar Kantin Fodio dake garin Sakkwato.
Bugu da kari Tambuwal ya shaida ma Alkalin Kotun, Abubakar Adamu cewa laifin da ake tuhumar mutanen biyu da aikatawa ya ci karo da sashi na 97 da na 284 na kundin hukunta laifuka, sai dai Dan Achabar ya musanta laifin, amma karamin yaro ya amsa.
Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, sai Alkali Abubakar ya bada umarnin daure mutanen biyun a gidan Kurkuku sakamakon bas hi da hurumin yin shari’a a wannan kara, sa’annan ya dage karar zuwa ranar 11 ga wata Yuni don mika ta ga wata Kotun dake da hurumin yin hukunci.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng