Wani basaraken musulmi a kudu ya yi umarnin rushe wasu gumaka da jama'a ke bauta
- Otarun Auchi, Mai martaba Alhaji Aliru Momoh, Ikelebe II ya bayar da umurnin a rushe dukkan wuraren bautan gumaka da ke masarautarsa
- Wasu matasan musulmi ne aka daura wa alhakin rushe wuraren bautan gumakan a kauyuka 25
- Basaraken ya bayar da umurnin ne bayan ya samu rahotanni cewa wasu musulmai a masarautar suna bautan gumaka
An bayar da umurnin rushe dukkan wuraren bautan gumaka da ke masarautar Auchi na jihar Edo. Mai martaba, Otarun Auchi, Alhaji Aliru Momoh, Ikelebe III ne ya bayar da umurnin.
Basaraken ya bayar da wannan umurnin ne bayan ya samu labarin cewa wasu daga cikin musulmi a masarautan suna bautan gumaka.
Fadar sarkin ta daura alhalkin zartar da wannan umurni ne a ga tawagar wasu matasa musulmi wanda za su kone dukkan wuraren bautan gumaka da suka samu a wasu kauyuka guda 25 da ke masarautar kamar yadda jaridar vanguard ta ruwaito.
Legit.ng ta gano cewa Otaru ya bayar da sanarwan ne a jawabin da yayi a taron majalisar masu bashi shawara wanda akayi a fadar sa a karshen makon da ya wuce.
KU KARANTA: Ta shiga haukan da gan-gan don kada ta biya kudin mota
Dan iyan Auchi, Yarima Usman Abudah ya tabbatar da umurnin. Ya kuma yi gargadi ga matasan sun bambance tsakanin wuraren tarihi da wuraren bautan gumaka saboda su guje wa yin barna wajen gudanar da aikin.
"Abinda fadan ke kira ga mutane shine su dena kawo bidi'a cikin addini, duk wata matsala da ke damun mutum, Allah ne kadai zai iya warware masa matsalar amma bai wai mutum ya rika ikirarin musulunci ba amma kuma ya koma gefe guda yana aikata wasu bidi'o'in, hakan ya sabawa addinin musulunci. Wannan abu ne mara kyau kuma irin wannan matsalar ake fuskanta wajen safarar mutane."
A wata rahoton, Legit.ng ta ruwaito cewa basaraken garin Auchi, Mai martaba Alhaji Aliru Momoh, Ikelebe III ya ce wahalhalun da mutane ke fuskanta a farko mulkin shugaba Muhammadu Buhari za su zama alheri daga baya.
Basaraken ya fadi hakan ne yayin da gwamnan jihar, Godwin Obaseki da mataimakin sa suka ziyarci shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng