Gardin Malamin da ya jawo aka datse hannayen almajirin sa ya gamu da fushin kuliya
Kotu ta yankewa wani malamin makarantar allo, da ya yi sanadiyyar lalacewar hannayen wani karamin almajirin sa, hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari.
An yanke hannun yaron, Zubairu Abubakar, mai shekaru 12 bayan lalacewar hannayen sa sakamakon wani danyen hukunci da malamin nasa yayi masa bayan an zarge shi da satar waya.
Wasu ‘yan Najeriya da suka bayyana ra’ayin su a kan wannan hukunci sun ce hakan ya yi daidai domin zai zama tamkar gargadi ga masu yin mugunta a kan kananan yara.
Gwamnatin jihar Gombe c eta dauki nauyin dawainiya da biyan kudin magungunan yaron yayin da aka kwantar das hi a asibiti. Kazalika kungiyoyin kare hakkin bil’adama da na kula da ‘yancin dan adam sun tallafawa yaron.
DUBA WANNAN: Daya daga cikin tsofin gwamnonin Najeriya ya fice daga APC
A wani labarin na Legit.ng kun ji cewar, kotun kungiyar musulmi ta al-shabab dake kasar Somalia ta jefe wata mata har saida ta mutu.
An jefe matar ne saboda ta auri namiji fiye da daya, kamar yadda wani shafi mai alaka da kungiyar ya sanar.
Matar, Shukri Abdullahi Warsame, ta auri maza II ba tare da mutuwar aure tsakanin ta da namji koda daya daga cikin su ba.
Mayakan kungiyar al-shabab sun tona rami har wuya inda suka saka matar suka binne kafin su jefe ta har lahira a garin Sabale dake yankin Lower Shabelle.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng