Da dumin sa: Daya daga cikin tsofin gwamnonin Najeriya ya fita daga APC

Da dumin sa: Daya daga cikin tsofin gwamnonin Najeriya ya fita daga APC

Tsohon gwamnan jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola, ya fice daga jam’iyyar APP mai mulkin Najeriya da jihar sat a Osun.

Tsohon sakataren gwamnatin jihar Osun lokacin mulkin Oyinlola, Alhaji Kazeem Adio, ya tabbatar ga hakan a wata hira ta wayar tarho da gidan jaridar Daily Trust.

Adio, daya daga cikin na hannun daman tsohon gwamnan kuma yaron san a siyasa, ya bayyana cewar Oyinlola ya fice daga jam’iyyar tare da dukkan magoya bayan sa, saidai bai bayyana jam’iyyar da maigidan nasa ya koma ba.

Da dumin sa: Daya daga cikin tsofin gwamnonin Najeriya ya fita daga APC
Olagunsoye Oyinlola

Ina mai tabbatar maku cewar tsohon gwamna Oyinlola ya bar jam’iyyar APC tare da magoya bayan sa. Daga yanzu mu ba ‘ya’yan jam’iyyar APC bane. B azan yi Magana a kan jam’iyyar da zamu koma ba yanzu,” a cewar Adio.

DUBA WANNAN: Sojoji sun kashe sojan da ya bar aiki saboda an tura shi Maiduguri

Dama dai anyi has ashen fitar Oyinlola daga jam’iyyar APC tun bayan day a zama sakataren kungiyar Obasanjo mai kokarin kafa wata sabuwar gwagwarmaya a siyasance da zata buga da jam’iyyun APC da PDP.

A shekarar da ta gabata ne shugaba Buhari ya nada Oyinlola a matsayin shugaban masu kula tare das aka idanu a kan aiyukan hukumar bayar da katin shaidar dan kasa (NIMC).

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel