El-Rufai ya gargadi ma'aikatu akan korar 'yan NYSC

El-Rufai ya gargadi ma'aikatu akan korar 'yan NYSC

- Matsalar masu bautar kasa a wannan lokacin shine su samu wurin da zasu yi aikin su na shekara daya da hukumar take bayarwa

- Sai dai kuma da yawan ma'aikatu idan an tura musu masu bautar kasar basa karbar su

- Dalilin da yasa gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasir Ahmad El-Rufai ya gargadi ma'aikatu akan irin halayen da suke nunawa akan masu bautar kasar a fadin jihar

El-Rufai ya gargadi ma'aikatu akan korar 'yan NYSC
El-Rufai ya gargadi ma'aikatu akan korar 'yan NYSC

Gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasir Ahmad El-Rufai ya gargadi ma'aikatun gwamnati dana al'umma dake cikin jihar Kaduna akan korar masu Bautar Kasa da suke yi idan aka tura su domin gabatar da ayyukan su na shekara daya.

DUBA WANNAN: Ji ku qaru: Banbanci tsakanin Gurguzu da Jari Hujja

Da yake jawabi a lokacin da masu bautar kasar suka kammala atisayen su na sati uku, wanda ya samu halartar masu bautar kasa 2,200, gwamnan ya bada shawarar cewar, maimakon korar su da wasu ma'aikatun suke yi kamata yayi su taimaka masu su samu wararen da zasu bada gudummawar su domin kawo cigaban kasar nan baki daya.

El-Rufa'i wanda ya samu wakilcin sakataren jiha akan harkokin wasanni da al'adu, Alhaji Musa Adamu, ya jaddada cewa gwamnati baza ta yarda da korar masu bautar kasan da wasu ma'aikatun suke yi ba, saboda hakan ya sabawa dokokin da suka saka aka kafa kungiyar NYSC.

A farkon jawabin sa, shugaban hukumar NYSC na jihar Kaduna, Alhaji Dahunsi Mohammed ya roki gwamnati ta samar da karin wuraren kwana ga masu bautar kasar, saboda yawan da masu bautar kasar keda shi a wannan lokacin a cikin jihar Kaduna.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng