An Lakadawa Wani Barawon Nama duka har Lahira a kasar Zimbabwe
Rahotanni da sanadin shafukan jaridun The Punch da PM News sun bayyana cewa, wani mai babban kanti tare da ma'aikatan sa sun gurfana gaban kuliya da laifin lakadawa wani mutum duka har lahira a sanadiyar satar tsokar nama.
A ranar Juma'ar makon da ta gabata ne wannan mamaci Israel Mashinge, ya shiga babban kantin inda ya dirfafi bangaren da ake ajiyar nama ya kuma dauki wata babbar tsoka da ya lankaya ta cikin wandon sa ba tare da sanin na'ura mai daukar hoto na kallace da shi ba.
Yayin ficewa ma'aikatan wannan kanti suka yi masa tara-tara kuma suka sakaya shi cikin wani rukuni na kantin inda kowanen su ya tafki rabon sa.
KARANTA KUMA: Farashin Man Fetur ya tumfaya a Kasuwannin Duniya, Amurka ta janye alakar ta da Kasar Iran
Bincike ya tabbatar da cewar wadanda ake zargi sun sanya shi cikin wata mota kirar Toyota Hiace inda suka jibge shi a kusurwar wata babbar hanya bayan sun galabaitar da shi inda daga bisani ya cika a nan.
Legit.ng ta fahimci cewa, an tsinci gawar Israel ne da misalin karfe 5.00 na safiyar ranar 5 ga watan Mayu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng