Bayan ya biya mata kudin karatu har digiri, ta sake shi saboda wai shi bai yi makaranta ba
- Wata mace ta saki mijinta da suka kwashe shekaru 10 suna zaman aure tare
- Matar tayi ikirarin cewa mijin nata jahili ne
- An gano cewa mijin nata ne ya dauki nauyin karatun ta tun daga makarantar sakandire zuwa jami'a
Wata mace 'yar kasar Zambia mai suna Maria Tembo ta saki mijinta wanda ya dauki nauyin dawainiyar karatun ta na tsawon shekaru 10 da suke aure. Matar ta shaidawa kotu cewa baza ta iya cigaba da zama da mijin ta ba saboda shi jahili ne.
An gano cewa mijin nata mai suna Vincent ne ya biya mata kudin makaranta tun daga aji na uku na karamar sakandire har zuwa karatun ta na jami'a.
KU KARANTA: Abun kunya: An kama magidanci ya saci tukunyar miya
Tembo ta shaidawa kotu cewa tana son a raba auren ta da mijinta ne don kawayenta suna mata gori a kan cewa tana auren jahili. Rahotanni sun ce ta raba aurenta dashi ne kuma ta auri wani mutum da suka hadu a jami'a.
Kamar yadda kafafen yadda labarai na Zambia suka ruwaito, Vincent da Maria sunyi aure ne a shekarar 1997 kuma a shekarar 1995, Vincent ya taba sayar da gidansa saboda ya biya wa Maria kudin makaranta.
Kotun ta amince da bukatar Maria inda aka raba aurensu kuma aka umurceta ta biya tsohon mijin ta K10,000 (N359,600) saboda ya huce zafin rabuwa da ita da kuma sadaukar da shekaru 10 na rayuwarsa saboda ita.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng