Ana mutunta Najeriya a duniya ne saboda Buhari
- Wani yayi ikirarin cewa Shugaba Buhari ne dalilin da yasa kasashen suniya ke mutunta Najeriya
- Dr. Orji Uzor Kalu ne ya furta wannan magana yayin da ya ke hira da manema labarai a Legas
- Ya ce shugabanin kasashen duniya sun gamsu da irin ayyukan da shugaba Buhari ke yi a Najeriya
Tsohon gwamnan jihar Abia, Dr. Orji Uzor Kalu ya ce kasashen duniya na mutunta Najeriya ne saboda gaskiya da rikon amana tare kuma da tsare-tsare masu amfani da shugaba Muhammadu Buhari ke aiwatar wa a kasar.
Kalu yayi wannan maganar ne a jiya Laraba yayin da yake hira da manema labarai a Lagos inda ya kara da cewa ziyarar da shugaba Buhari ya kai kasar Amurka mabudin alheri ne ga kasar.
KU KARANTA: Kungiyar musulmi ta JNI ta baiwa gwamnati wata shawara game da haramta kodin
Ya bayyana cewa shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya gayyaci Buhari ne makonni kadan bayan Farai Ministan Theresa May ta gana da shugaba Buhari a kasar Landan kamar yadda NAN ta ruwaito.
Legit.ng ta gano cewa Kalu ya ce: "Gayyatar da shugabanin duniya ke yiwa shugaba Buhari alama ce da ke nuna sun gamsu da irin kokarin da ya ke yi na kawo gyara da cigaba a Najeriya."
Jigon na jami'iyyar APC ya kuma ce gwamnatin Buhari tana aiki babu kama hannun yaro wajen habbaka tattalin arzikin Najeriya kuma a halin yanzu wasu yan Najeriya sun fara ganin alamu cigaban da ake samu.
Tsohon gwamnan ya kuma shawarci matasa su cigaba da aiki tukuru don kawo cigaban da muke bukata a kasar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng