Da dumin sa: Majalisar dattijai zata dauki tsatstsauran mataki a kan Sifeton 'yan sanda, sun shiga ganawar sirri
Yanzu Sanatocin Najeriya sun shiga wata ganawa ta sirri domin daukan mataki a kan babban Sifeton hukumar 'yan sanda ta kasa, Ibrahim Idris.
A yau ne, Laraba, majalisar take saka ran bayyana Idris a zauren majalisar domin amsa wasu tambayoyi a kan batun tsaro da kuma kama abokin aikin su, Sanata Dino Melaye.
Saidai a karo na uku, Sifeton yaki ya bayyana a gaban majalisar sannan bai tura wakilci ba.
A baya, Sifeto janar din ya aike da mataimakin sa, Habila Joshak, domin ya wakilce shi amma majalisar taki amincewa da hakan.
DUBA WANNAN: Bikin wasan gargajiya ya firgita jama'a a jihar Legas, Bankuna sun rufe, mata sun buya a gida
Masu hasashen lamuran gwamnati na ganin cewar za a shiga takun saka tsakanin majalisar da shugaban hukumar 'yan sanda, Ibrahim Idris.
Ana hasashen cewar shugabannin majalisun kasar nan sun kai karar Sifeto Idris wurin shugaba Buhari yayin wata ganawa da suka yi a daren shekaranjiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng