Dan jaridar Najeriya ya lashe wata gagarumar gasa ta marubutan duniya

Dan jaridar Najeriya ya lashe wata gagarumar gasa ta marubutan duniya

Wani Dan jaridar Najeriya, Abubakar Ibrahim, ne ya lashe wata gagarumar lambar yabo na marubuta a duniya mai suna Michael Elliot Award saboda rahotannin da ya rubuta akan adadin mutanen da suka rasu ko rasa muhallinsu sakamakon ta'addancin Boko Haram.

Cibiyar yan jarida na kasa da kasa (ICFJ) ta ce an zabe Ibrahim ne wanda marubuci ne da ke aiki da jaridar Daily Trust na Najeriya daga cikin mutane 238 da suka shiga gasar daga kasahen duniya daban-daban.

Dan jaridar Najeriya ya lashe wata gagarumar gasa ta marubutan duniya
Dan jaridar Najeriya ya lashe wata gagarumar gasa ta marubutan duniya

An kirkiri wannan lambar yabon ne daraja ne a shekarar 2016 don karama marigayi Michael Elliott inda cibiyar yan jaridar na kasa-da-kasa tayi hadin gwiwa da iyalan mamacin. Elliot gogagen dan jarida ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen rubuta labarai don habbaka rayuwar dan-adam.

DUBA WANNAN: Ga araha ga amfani: Fa'idoji 6 dake tattare da cin dabino

Mercy Juma, ne kasar Kenya da ke aiki da BBC a matsayin mai kawo rahoto a fanin kiwon lafiya ne ta fara lashe lambar yabon karo na farko a shekarar saboda gudunmawar da ta bayar wajen habaka aikin jarida a duniya.

An wallafa rahoton da Ibrahim ya rubuta mai taken, 'All That Was Familiar', a mujallar Granta a watan Mayun 2017.

A labarin, ya yi bincike inda ya gabatar da yadda al'umma ke rasa rayyukansu sakamakon ta'addancin kungiyar na Boko Haram wanda mutane sai dai suji kawai ana kidayar wadanda suka mutu ba tare da sanin ko su wanene ba.

Sama da mutane miliyan biyu ne suka rasa muhallinsu sakamakon ta'addancin kungiyar a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, Kudancin Nijar da kuma Arewacin Kamaru.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel