Kamar an yi an gama: Real Madrid za ta dauke Salah daga Liverpool

Kamar an yi an gama: Real Madrid za ta dauke Salah daga Liverpool

- Hatsabibin ‘Dan wasan Firimiya zai koma taka leda a kasar Sifen

-Babban 'Dan wasa Salah ya shirya barin Liverpool zuwa Madrid

- Real na neman sayen Salah da kuma Neymar daga Kungiyar PSG

Dan wasan Kungiyar Liverpool da yayi fice bana watau Mohammed Salah na daf na barin Gasar Firimiya ya koma taka leda a kasar Sifen. Yanzu maganar komawar sa Birnin Madrid tana daf da tabbata.

Kamar an yi an gama: Real Madrid za ta dauke Salah daga Liverpool
'Dan wasa Mohammed Salah zai koma Real Madrid bana

Mun samu labari daga Jaridun Kasar Sifen cewa Mohammed Salah ya amince zai koma buga wasa a Madrid daga kakar bana. ‘Dan wasan mai shekara 25 zai kuma kara da Real Madrid a wasan karshe na Gasar Champions league.

Rahotannin da ke yawo daga Jaridar Dob Balon na kasar Sifen shi ne ana tunanin ‘Dan wasa Mohammed Salah zai bugawa Liverpool wasan karshe a karawar su na cin kofin Gasar Zakarun Nahiyar Turai a karshen wannan watan.

KU KARANTA: Rikici ya barke tsakanin Jami'an tsaro a Garin Legas

Ko da dai har yanzu maganar ba ta fito fili ba amma ba mamaki Kocin na Liverpool ya nemi fam Miliyan €200 daga Real Madrid kafin su raba shi da Tauraron ‘Dan wasan gaban na sa wanda ya ci kwallaye sama da 40 a shekarar nan.

Akwai kishin-kishin din cewa Shugaban Kungiyar Real Madrid watau Florentino Perez na neman sayen Mohammed Salah da kuma ‘Dan wasan gaban PSG watau Neymar Jr. domin duk su rika buga wasa tare da Cristiano Ronaldo a Kulob din.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel