Gwamnan Borno ya jagoranci taron Gwamnonin Yankin da Boko Haram ya shafa

Gwamnan Borno ya jagoranci taron Gwamnonin Yankin da Boko Haram ya shafa

- Wasu Gwamnonin Najeriya da na Nijar sun hadu a wajen wani taro

- Kungiyar Gwamnonin da ke Yankin Tafkin Chadi sun gana a Borno

- Gwamnonin da rikicin Boko Haram ya shafa dai su na neman mafita

Gwamnonin Jihohi da dama na Kasashen Najeriya da ma Makwabatan su na Kasar Jamhuriyyar Nijar sun yi wani babban taro a Najeriya domin farfado da Yankin na tafkin Chad inda Boko Haram su ka yi ta’asa na tsawon shekaru.

Gwamnan Borno ya jagoranci taron Gwamnonin Yankin da Boko Haram ya shafa
Hoton taron Gwamnonin Yankin daga UNDP

Yerwa Express ta rahoto cewa Gwamnonin kasashen na Afrika da ma Gwamnatin kasashen Turai irin su Jamus sun gana ne a wajen wani taro da Jihar Borno ta shirya da sa hannun Hukumar UNDP ta Majalisar Dinkin Duniya.

Gwamna Kashim Shettima da Takwaran sa na Jihar Yobe da Adamawa sun yi taro tare da Gwamnonin Jihar Diffa da kuma Zinder a cikin Nijar. Bayan nan kuma an gana da Gwamnatocin Kasar Jamus da Norway da Suwidin a zaman.

KU JARANTA: Ba na jin dadin abubuwan da ke faruwa a irin su Benuwe da Zamfara – Shugaba Buhari

A wajen taron an tattauna game da yadda Boko Haram tayi barna a Yankin inda yayi kira da a hada hannu domin kawo karshen ta’adin. Kasashen Yankin za su kara hada-kai da ba juna bayanan da za su taimaka wajen yaki da Boko Haram.

A jawabin na Gwamnan Borno kashim Shettima ya kuma nemi a samawa wadanda ke gudun hijira a Yankin mafita. An dai kafa Kungiya ta Gwamnonin Kasashen da ke Yankin na tafkom Chadi domin samun maganin matsalolin Yankin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel