Saba dokar Allah: Kotun shari'ar Musulunci ta sa an tsalalawa wani magidanci bulala 5

Saba dokar Allah: Kotun shari'ar Musulunci ta sa an tsalalawa wani magidanci bulala 5

Wata kotun shari'ar Musulunci dake Magajin Gari a garin Kaduna tayi umarnin a tsalalawa wani magidanci, Idris Sa'idu, bulala biyar saboda yiwa aure rikon sakainar kashi.

Alkalin kotun, Mallam Dahiru Lawal, ya umarci magidanci ya biya matar sa, Hauwa Abdullahi, N5k saboda ya wulakanta ta tare da bata mata lokaci.

Alkalin ya yanke wannan hukunci ne bayan magidanci ya furta garangatsai cewar "na saki mata ta saki uku" a gaban kotu. Furucin da alkalin kotun ya ce ya saba da shari'ar Musulunci.

Saba dokar Allah: Kotun shari'ar Musulunci ta sa an tsalalawa wani magidanci bulala 5
Saba dokar Allah: Kotun shari'ar Musulunci ta sa an tsalalawa wani magidanci bulala 5

Tunda farko, matar mutumin, Hauwa, ta shigar da korafin mijin gaban kotun cewar, ya kore ta daga gidan sa tun shekarar da ta wuce kuma ba tare da ya taba waiwayen halin da take ciki ba.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kai hari jami'a a Abuja, sun sace lakcara

Hauwa ta shaidawa kotu cewar mijin nata ba sakinta ya yi ba, kawai ya kore ta ne tun azumin bara.

Da yake mayar da martani, Sa'idu, ya ce ya kori matar sa, Hauwa, ne saboda tana yin waya da tsohon saurayin ta, lamarin da ya ce ba zai yarda da shi ba, kuma nan take ya furta cewar ya sake ta saki uku.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel