Yaki da ta’addanci: Dakarun Sojojin Najeriya suna tserewa da yan mata a yankin tafkin Chadi
Al’umma mazauna yankin tafkin Chadi sun koka kan wasu gurbatattun halaye da Sojojin Najeriya ke aikatawa a yankin nasu, inda aka tura su da nufin yaki da kungiyar ta’addanci na Boko Haram, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Al’ummomin tafkin Chadi sun zargi Dakarun Sojin Najeriya da dauke musu yara mata daga kauyukansu tare da tserewa dasu, inji wani rahoto da hukumar cigaban kasashen Duniya, UNDP ta majalisar dinkin Duniya ta fitar.
KU KARANTA: An sake kwatawa: Sojoji sun cika hannayensu da wasu yan bindiga guda 6 a jihar Benuwe
“A kasar Kamaru, dangantaka tsakanin Sojoji da mazauna yankin ya ta’allaka ne kawai ga zinace zinace da yan matansu, tare da cin mutuncin yan matan da Sojoji ke yi, misali ko a kauyen Limani, sai da aka samu wata mata da wani Soja ya dirka mata ciki, inda ta haifi da namiji, wannan yayi sanadiyyar koranta daga gidansu sakamakon abin kunya ne a wajensu.” Inji rahoton.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito akwai yan mata dayawa da suka bi Sojoji ba tare da cika ka’idojin aure ba, hakazalika Sojojin suna kwatar kudade daga hannun mutanen kauyukan musamman a shingen bincike.
Sai dai duk da wannan ta’asa da Sojoji ke tafkawa, rahotan ta bukaci da a turo karin Dakarun Soji zuwa yankunan, wadanda suka goge, kuma suka san makaman aiki don tabbatar da tsaro, sa’annan ta bukaci hukumomi da su tabbatar cewa Sojoji na bin ka’aidar aiki.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng