'Yan bindiga sun kai farmaki jami'a a Abuja, sun yi awon gaba da lakcara
A jiya, Litinin, wasu 'yan bindiga suka kai farmaki wata jami'ar Abuja, Veritas University, tare da yin awon gaba da wani lakcara.
'Yan bindigar sun shiga ginin kiristoci na Katolika dake cikin jami'ar tare da yin harbin iska kafin daga bisani su shiga gidan malamin jami'ar dake makwabtaka da ginin.
Malamin jami'ar da suka sace ya kasance daya daga cikin limaman Cocin makarantar sannan mai taimakawa na musamman ga shugaban jami'ar, Farfesa Michael Kwanashie.
Daya limamin Cocin da suke zaune gida daya da lakcaran da aka sace ya samu nasarar kubuta ta hanyar buya a cikin rufin gidan da suke.
DUBA WANNAN: Hanyoyi biyu da motsa jiki ke yiwa lafiya lahani
Wata dalibar makarantar mai suna Mbafan ta bayyana cewar sun firgita da jin harbe-harbe a makarantar da misalin karfe 12 na dare amma saida safe ne suka san cewar an sace malamin na su. 'Yan bindigar na neman Naira miliyan N kudin fansa.
Shugaban jam'iar, Farfesa Kwanashie, ya ki furta komai kan batun saboda dalilan tsaro, kamar yadda ya bayyana.
Kakakin hukumar 'yan sanda a birnin tarayya, Abuja, Anjuguri Manzah, ya ce zai nemi karin bayani daga ofishin 'yan sanda dake Bwari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng