Kungiyar Izala ta ziyarci ofishin gwamna Bello, ta jinjina masa a kan wani namijin kokari

Kungiyar Izala ta ziyarci ofishin gwamna Bello, ta jinjina masa a kan wani namijin kokari

Shugabancin kungiyar Izalatul-Bid'a-Wa-Iqamatus-Sunnah na kasa karkashin jagorancin, Sheikh Sani Yahaya Jingir, ta ziyarci ofishin gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello.

Kungiyar t ziyarci gwamnan ne jiya, Litinin, a ofishin sa dake garin Minna, babban birnin jihar Neja.

Kungiyar ta yabawa gwamnan bisa cigaba da aiyukan raya kasa da gwamnatocin baya basu kammala ba.

Kungiyar Izala ta ziyarci ofishin gwamna Bello, ta jinjina masa a kan wani namijin kokari
Gwamna Abubakar Bello da Sheikh Jingir

Kungiyar ta kara da cewa, ta ziyarci gwamnan ne domin bashi karfin gwuiwa a kan irin aiyukan da gwamnatin sa ke shimfidawa jama'a bayan dorawa a kan aiyukan da ya gada.

Kungiyar ta Izala ta bayyana cewar tana goyon bayan gwamnatin gwamna Bello saboda ta bawa bangaren ilimi da makarantu muhimmanci.

DUBA WANNAN: An gano dalilin da yasa yaki da cin hanci da Buhari keyi baya samun nasara

Kazalika kungiyar tayi kira ga iyaye da su tura yara makarantu dake kusa da su sabanin tura su makarantun nesa inda zasu zama mabarata.

Sheikh Jingir ya yi kira ga 'yan Najeriya da su zauna lafiya da juna domin samun cigaba a kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng