An kara kama shi da laifin fashi da makami kwana 25 da sakin sa daga gidan yari

An kara kama shi da laifin fashi da makami kwana 25 da sakin sa daga gidan yari

- Hukumar Yan sanda sun sake kama wani dan fashi da makami bayan fitowarsa daga gidan yari cikin kwanakin nan

- Dan fashin Ahmed Adewole wanda akafi sani da fatalwa ya ce ya koma harkarsa ta fashin ne don bai iya wata sana'a ba

- Ya sanar da manema labarai cewa aka masa kirari da fatalwa ne saboda yanayin yadda yake fashi cikin hanzari da tsanaki

Hukumar 'Yan sandan jihar Legas ta sake cafke wani gawurtaccen dan fashi da makami, mai suna Ahmed Adewole wanda akafi sani da 'Spirit' wato fatalwa wanda ya fito daga gidan yari a ranar 11 ga watan Afrilun 2018 amma kuma gashi ya cigaba da halinsa na da.

An kara kama shi da laifin fashi da makami kwana 25 da sakin sa daga gidan yari
An kara kama shi da laifin fashi da makami kwana 25 da sakin sa daga gidan yari

Rahotanni sun nuna cewa kafin zuwansa gidan yari, Adewole yana daya daga cikin 'yan fashin da hukumar Yan sanda ke nema ruwa a jallo kuma an cigaba da nemansa bayan fitowarsa saboda an sami rahotannin ya cigaba da halin nasa.

KU KARANTA: Babu wani sauran gari da ke hannun Boko Haram: Najeriya ga Majalisar Dinkin Duniya

A wata hira da ya yi da manema labarai, 'Spirit' ya amsa cewa ya dade yana yiwa mutane fashi da makamai. Ya ce, " Ni dan fashi ne, na dade ina yiwa mutane fashi da karamar Pistol da ake kera a gargajiyance.

"An kama ni da farko ne a Mushin lokacin da yan sanda ke sintiri kuma na tafi gidan yari na watanni shida, na fito daga gidan yari ne a ranar 11 ga watan Afrilu."

Ya kuma shaidawa manema labaran cewa ya koma mumunar harkarsa ta fashi da makami ne bayan wani abokinsa mai suna Rashidi Garuba ya janyo hankalinsa tunda bashi da wata sana'a da zaiyi bayan ya fito daga gidan yarin.

Adewole ya shaidawa manema labaran cewa abokansa na kiransa fatalwa ne saboda yadda yake gudanar da fashi da makaminsa cikin hanzari da tsanki kamar fatalwace ke yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164