Ina gwanin wani ga nawa: Wani hamshakin Farfesan jami’ar ABU ya samar da maganin zazzabin cizon Sauro

Ina gwanin wani ga nawa: Wani hamshakin Farfesan jami’ar ABU ya samar da maganin zazzabin cizon Sauro

Wani hamshakin Farfesa a sashin kimiyyar hada magunguna na jam’iar Bayero dake garin Zaria, cikin jihar Kaduna, Farfesa Umar Katsayal ya samar da wasu magungunan zazzabin cizon Saura masu matukar inganci, inji rahoton Kamfanin dillancin Labaru, NAN.

Katsayal ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 7 ga watan Mayu a garin Sandamu dake gab da garin Daura, inda yace ya samar da wadanann magunguna ne daga sauyan wata shuka da ta dade tana maganin cututtukan da suka shafi asma, tari, sanyi, kiba da cizon maciji, da kuma bayan wani shuka da ake kwalliyar gida da ita.

KU KARANTA: Harin Birnin Gwari: Rundunar Soji za ta girke Dakarun dindindin a Birnin Gwari – El-Rufai

Ina gwanin wani ga nawa: Wani hamshakin Farfesan jami’ar ABU ya samar da maganin zazzabin cizon Sauro
Farfesa Umar Katsayal

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Farfesan yana cewa an samar da magungunan ne bayan wani gwaje gwaje a dakunan gwajin inganci da illolin magunguna, don tabbatar da sahihancinsu, ya kara da cewa nan gaba kadan zasu shigar da maganin kasuwa bayan cika duk sharuddan siyar da magani.

“Munyi shekara da shekaru muna gudanar da binciken ilimi game da wannan magunguna, zamu kara zage damtse don ganin mun samar da magunguna da dama.” Inji Katsayal.

Ina gwanin wani ga nawa: Wani hamshakin Farfesan jami’ar ABU ya samar da maganin zazzabin cizon Sauro
Shukokin

Farfesa Katsayal wanda tsohon dan majalisar wakilai ne dake wakiltar karamar hukumar Sandamu, Daura da Maiadua ya yaba ma shugabancin jami’ar da ta bashi da damar cimma wannan gagarumar nasara,

Daga karshe ya yi kira ga takwarorinsa Malaman Jami’a dasu dage su zage karfi wajen samar ma al’umma hanyoyin shawo kan matsalolinsu a ilimance ta hanyar gudanar da bincike binciken ilimi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel