Zabukan cikin gida naAPC: wani Ministan Buhari ya tsallake rijiya da baya a hannun fusatattun matasa

Zabukan cikin gida naAPC: wani Ministan Buhari ya tsallake rijiya da baya a hannun fusatattun matasa

Saura kiris wasu fusatattun matasa a jihar Anambra su afka ma wani Minista a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Chris Ngige, ministan kwadago, a ranar Lahadi, 6 ga watan Mayu, inji rahoton jaridar The Cables.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a yayin taron sulhu da aka gudanar a garin Awka don a sulhunta tsakanin wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar da basa ga Maciji da juna a sakamakon zaben shwuagabannin jam’iyyar APC a matakin mazabu.

KU KARANTA: Wani Barawo ya mika kansa ga Yansanda bayan buhun gyadan da ya sata ya makalkale masa a wuya

Rikicin ta taso ne lokacin da wasu yayan jam’iyyar suka fara iface iface suna fizge fizge kan cewa ba ayi musu adalci ba, inda suke zargin Ministan da sauya sakamakon zaben da ya gudana don biyan bukatunsa.

Zabukan cikin gida naAPC: wani Ministan Buhari ya tsallake rijiya da baya a hannun fusatattun matasa
Nigige

Daga nan ne fa matasan suka nemi su kassara Minista, Allah ya kiyaye akwai jami’an tsaro a taron, inda suka kare minstan ta hanyar harbe harbe a sama, shi kuma ministan ya ranta ana kare, ya afka cikin Mota, sai gida.

A jawabinsa kafin tashin taron, tsohon dan takarar gwamnan jihar, kuma dan majalisa mai ci a yanzu, Tony Nwoye ya bayyana cewa: “Mun ji kunya a matsayinmu na jam’iyya, amma ba zamu bari wasu yan tsiraru su sanya jam’iyyar nan a cikin aljihunsa ba. Akwai kwamitin da aka kafa su gudanar da zaben, sai a ranar Lahadi suka iso, amma Ngige na fada mana wai sun yi zabe tun ranar Asabar, bai isa ba.”

Sai dai Minista a Nigige ya mayar da martani, inda ya musanta zarge zargen da Nwoye ke yi masa, kuma ya bayyana zabukan a matsayin takara tsakanin yan uwa, daga karshe yace: “Aikinmu ne mu tabbatar da bukatar jam’iyyarmu.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng