Abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da kodin

Abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da kodin

Haramta hadawa da sayar da maganin tari mai dauke da kodin da gwamnatin tarayya tayi a ranar 1 ga watan Mayu ya janyo gamu da ra'ayoyi daban-daban daga 'yan Najeriya, yayin da wasu ke jinjinawa gwamnati wasu kuma na ganin kamata yayi ayi bincike na a gano masu sayar dashi ba bisa ka'ida ba.

Ministan lafiya na kasa, Isaac Adewole, wanda ya bayar da sanarwan, ya ce matakin da gwamnati ta dauka ya zama dole ne saboda yadda wasu 'yan Najeriya ke amfani dashi ba bisa ka'ida ba.

A shekarar 2016, wata cibiyar bincike ta fitar da wani rahoto wanda ke nuna yadda kodin da wasu kwayoyi ke lalata rayuwar matasa musamman na Arewacin Najeriya.

Ga wasu muhimman abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da yaduwar amfani da kodin ba bisa ka'ida ba a Najeriya.

Abubuwa 10 da ya kamata ka sani a kan kodin
Abubuwa 10 da ya kamata ka sani a kan kodin

1) Kodin dai maganin ne rage radadin a jiki ciwo amma kuma mutum na iya zama ya dogara dashi. Tana iya kawo ciwon kwakwalwa da mantuwa, tana kuma iya janyo ciwon koda da wasu matsalolin.

2) Galibi dai matasa ne kan gaba wajen siyan kodin don su sha suyi maye. Wani abin mamaki kuma shine 'yan mata ma sun fi mazan sha, ciki har da masu juna biyu.

KU KARANTA: Anyi dauki ba dadi da jami'an NDLEA yayin da suka je kama wani dillalin miyagun kwayoyi

3) Daga kasashen waje ake sayo sinadrin na kodin, daga baya sai kamfanonin kera magunguna na Najeriya suyi amafani dashi wajen sarrafa maganin tari.

4) Ana sayar da kwalba daya ne daga N1000 zuwa N1200 kuma wadanda kawazucin shan kodin ya kama su sosai suna iya shan kwalba hudu a kowanne rana.

5) Duk da cewa an sayar dashi ba tare da izinin likita ba, zaka rika gani ana sayar da shi kuma matasa na zuba shi cikin lemun kwalba kamar coke kuma kaga matasan sun shan sa amma ba za ka gane ba.

6) Mafi yawanci masu shan kodin matasan arewa ne. Haramta shan giya a mafi yawancin jihohin arewa ne ke sa matasa shan kodin da wasu kwayoyi kamar tramadol, rephnol da wasu magungunan masu sanya maye.

7) Ana shan kwalaben kodin guda sama da miliyan uku a kowane rana a jihohin Kano da Jigawa kamar yadda Majalisar Dattawa ta bayyana.

8) Hukumar yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) tana cigaba da yaki da wannan matsalar. A wani kame da hukumar tayi, an kama kwalaben kodin 24,000 a wata mota guda daya a jihar Katsina.

9) Mawakan Najeriya suna daga cikin wadanda ke karfafawa matasa shan kodin saboda yadda suke ambatar shan kodin din a matsayin 'wayewa' a wasu wakokinsu.

10) Idan mashaya kodin din sun sha, takan sanya su jiri, maye, rashin jin zafi da gane-ganen wasu abubuwa da sauran mutane basu iya gani kamar yadda wasu masu matsalar kwakwalwa ke gani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel