Sojin saman Najeriya ta cika shekaru 54 da kafuwa, Kalli hotunan kayayakin yaki da suka mallaka
A jiya ne 4 ga watan Mayu NAF tayi bikin cika shekaru 54 da kafuwa, Hukumar ta bude taron ne da baje kolin hotunan kayayakin yaki na tarihi da ke nuna yadda hukumar ta samu cigaba cikin shekarun da suka gabata.
An gudanar da baje kolin hotunan ne a sansanin hukumar da ke garin kaduna inda ministan harkokin gida, Laftanat Janar Abdulrahaman Dambazau (murabus) ne babban bako.
Hukumar tayi amfani da wannan daman don nuna wa duniya irin bajinta da kwazo da injiniyoyin hukumar sojin ke nuna wa wajen wasu kere-kere masu ban sha'awa wanda hakan abu ne da yan Najeriya ya kamata suyi alfahari dashi.
Taron ya samu hallartan babban hafshin sojin sama CAS Air Marshall Sadique Abubakar tare da sauran manyan manyan sojojin Najeriya.
Cikin murnar cika sheakru 54, Hukumar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta kaddamar da sabbin jiragen yaki masu saukan angulu biyu kirar Mi-35M da gwamnatin tarayya ta sayo daga kasar Rasha.
Ana sa ran sabbin jiragen yakin zasu taimakawa sojojin Najeriya a yakin da sukeyi da yan ta'ada da ma kara inganta tsaro a wasu sassan kasar.
Jiragen sai sun iso Najeriya ne tun ranar Litinin 30 ga watan Afrilu inda aka ajiye su a sansanin sojin saman da ke Makurdi a jihar Benue.
Jiragen sun iya gani cikin dare kuma suna daga cikin jiragen yaki mafi da ake tunkaho da su a duniya.
Duk da haka gwamnatin tana jiran isowar wasu jiragen masu saukar angulu kirar Mi-35 wanda gwamnatin tarayya ta fara biyan kudinsu tun 2015.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng