Abin tausayi ya faru a Kano: Dalibi ya lume a ruwa garin ceton abokinsa
Wani abin bakin ciki ya faru a Jami'ar kimiyya da fasaha da na jihar Kano yayinda wani dalibi ya yi gamo da ajalinsa a rafin da ke garin Wudil.
Wani dalibi dan aji uku mai suna Farouk Abubakar ne ya tafi rafi tare da abokansa biyu a ranar Laraba 2 ga watan Mayu don suyi wanka amma ya rasu yayin da yake kokarin ceto abokinsa daga lumewa.
Daliban jami'an sun gudanar da zanga-zanga a kan rasuwar abokin karatunsu inda rahotanni suka bayyana cewa anyi kacha-kacha da wasu motocci da kayayaki a makarantar.
KU KARANTA: Kungiyar musulmi ta JNI ta bukaci jama'a su farga saboda jami'an tsaro sunyi sanyi
Wani abokin marigayin mai suna Moses Istifanus ya yi amfani da shafinsa na dandalin sada zumunta na Facebook inda ya jajantawa iyalan mamacin ta hanyar rubuta wani sako mai ratsa zuciya a shafin nasa.
Kalamansa: "Ina son inyi amfani da wannan dama don mika ta'aziyya ta ga iyalan Farouk Abubakar na jami'ar kimiyya da fasaha na jihar Kano. Jarumin da ya sadaukar da rayuwan sa don ya ceto abokinsa.
Anyi zanga-zanga, an lalata wasu kayayakin makaranta, anyi kacha-kacha da motocci duk saboda sakaci da kalaman kiyaya da shugaban kula da daliban makarantan ya ke furtawa. Amma babu wata zanga-zanga da za ta iya dawo mana da kai.
Allah ya sa ka huta.
Na fadi cewa kai jarumi ne saboda kayi sadaukar da rayuwarka saboda wani. Jarumai dama kullum an san su da rashin fargaba. Jarumai sune suke da karfin zuciyar aikata abubuwan da zasu kawo canji."
Jarumin mu, ba za mu taba mantawa da kai ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng