Bincike: Kashi 30 bisa 100 na mutuwar matasa cin jan-nama ke janyo ta
- Nama ya kasu ja da fari, jan nama yafi illa ga lafiya
- Farin nama bashi da illa sosai kamar jan nama
- Farin nama ya hada da tsuntsaye, da na ruwa
Masana a jami'ar Harvard ta kasar Amurka sun gano cewa cin jan-nama yana kisan matasa sosai a shekara, kamar yadda shan taba sigari ko giya ko qiba ke janyo wa. Wannan na nufin akwai mace-mace da a'a iya kaucewa na ba-gaira ba dalili.
A binciken, an gano za'a iya cetar Amurkawa akalla 200,000 da ke mutuwa daga cutuka da cin naman ke iya janyo wa.
Cutukan sun hada da kiba, maiko da Kwalestarol, sinadarin maiko mai sanya hawan jini da bugun zuciya.
DUBA WANNAN: Anyi min wahayi Buhari ba zai zarce ba
Ko a nan yankin mu na Afrika dai, muna cin nama sosai, kamar su balangu, tsire, suy da kilishi ko dambu, wanda akanyi da jan nama.
Farin nama dai yafi lafiya, kamar na tsuntsu ko na ruwa, kamar su kifi da qaguwa, kwado da maciji.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng