Rikici: Makarantun Firamare 64 sun shiga cikin tasku a jihar Nasarawa

Rikici: Makarantun Firamare 64 sun shiga cikin tasku a jihar Nasarawa

Mun samu rahoton cewa kimanin makarantu 64 na Firamare su ka shiga cikin halin kakanikayi a yankin Gabashin Birnin Lafia na jihar Nasarawa sakamakon rikita-rikita tsakanin Makiyaya da Manoma.

Babban sakataren ilimi na yankin, Yusuf Okbele, shine ya bayyana hakan a ranar yau ta Juma'a yayin horas da wasu malamai a birnin Lafiya.

A cewar sa, rikita-rikita a yankin Kudancin jihar ta dakusar da harkokin gudanar da karatu na makaratun firamare 64 dake birnin Lafia.

Rikici: Makarantun Firamare 64 sun shiga cikin tasku a jihar Nasarawa
Rikici: Makarantun Firamare 64 sun shiga cikin tasku a jihar Nasarawa

Sai dai ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ta na iyaka bakin kokarin ta wajen babbago da habakar harkokin karatu a yankin wanda a halin yanzu wasu makarantun sun ci gaba da gudanar da harkokin su kamar yadda suka saba.

KARANTA KUMA: Tsige Shugaba Buhari zai kawo koma baya a Najeriya - Gowon

Babban sakataren ya kirayi iyayen yara na yankin akan su tura 'ya'yayen su makaranta sakamakon zaman lafiya da ya fara wadatuwa tare da kiran malamai akan su nuna zakakuranci wajen sauke nauyin su da zai kawo ci gaba mai dorewa.

A yayin haka kuma jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya goyi bayan shugaba Buhari akan matsayar sa ta 'yan sandan jiha.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng