Zaben APC: Sanatan da aka dakatar a Kaduna yace ba za ta sabu ba

Zaben APC: Sanatan da aka dakatar a Kaduna yace ba za ta sabu ba

- Sanatan APC a Jihar Kaduna yace da shi za a fito zaben da za ayi gobe

- Sakataren APC na Kaduna ya gargadi Sanatan cewa an dakatar da shi

- Sanata Hunkuyi da sauran Sanatan Sanatoci ba su jituwa da Gwamnan

Sanatan Kaduna ta Arewa Sulaiman Othman Hunkuyi ya maida martani ga Sakataren Jam’iyyar APC na rikon kwarya a Jihar Kaduna Yahaya Baba Pate da yace ka da ya sake ya fito wajen zaben gobe. An dai dade ana rikici a Jam'iyyar a Kaduna.

Zaben APC: Sanatan da aka dakatar a Kaduna yace ba za ta sabu ba
Sanata Hunkuyi yayi kaca-kaca da Sakataren Jam’iyyar APC na Jihar Kaduna

Sulaiman Othman Hunkuyi ya bayyana cewa har yanzu shi rikakken ‘Dan Jam’iyya ne kuma babu abin da ya fitar da shi. Hunkuyi yace kwanan nan Shugabannin Jam’iyyar na kasa su ka kai masa ziyara don haka babu wanda ya dakatar da shi.

Sanatan na Kaduna yace Sakataren Jam’iyyar watau Yahaya Pate sojan gona ne don babu wanda ya san da zaman shi a Jam’iyyar. Asali ma dai yace an dakatar da shi na shekara guda da rabi saboda angulu da kan mage da yake yi wa APC.

KU KARANTA: ‘Yan Majalisu za su kara da Gwamnoni wajen zaben shugabannin APC

Jam’iyyar ta APC a Kaduna tace Sanatan da yanzu an dakatar da shi a Jihar ya rufawa kan sa asiri kar ya fito wajen zaben da za ayi gobe. Hunkuyi kuwa yace har gobe yana Jam’iyya don kuwa manyan APC irin su Segun Oni sun san da zaman sa.

Sanatan dai ya rufe da cewa kowa ya san cewa shi mutum ne mai bin doka da ka’ida a Jihar Kaduna. Gobe APC za ta gudanar da zaben ‘Ya ‘yan ta a Mazabu da Yankunan kasar nan inda ake tunani za a kara tsakanin Sanatan da Gwamnan Jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng