Shugaban INEC na so ‘Yan takara su rika tafka muhawara kafin zabe

Shugaban INEC na so ‘Yan takara su rika tafka muhawara kafin zabe

- Hukumar INEC na nema a rika muhawara kafin ayi zabe a Najeriya

- Shugaban INEC Mahmud Yakubu ya kawo wannan shawara kwanaki

- Atiku Abubakar dai kuwa yace hakan zai sa a gane shirin ‘Dan takara

Shugaban Hukumar INEC na zabe na kasa watau Farfesa Mahmud Yakubu ya bayyana cewa zai yi kyau ‘Yan takara su rika muhawara. Farfesa Yakubu ya bayyana wannan ne a wajen wani taro a Garin Legas.

Shugaban INEC na so ‘Yan takara su rika tafka muhawara kafin zabe
Shugaban Hukumar zabe na kasa INEC Farfesa Mahmud Yakubu

Farfesa Mahmud Yakubu yake cewa muhawara za ta taimaka wajen zaben nagari a tsarin damukaradiyya. Hakan dai zai ba masu zabe dama su san wanene ainihin na zaba tsakanin ‘yan takarar da su ke neman kujera.

KU KARANTA:

A taron da aka shirya Ranar Laraba, Shugaban INEC na kasa ya bayyana cewa muhawara za ta bada dama masu neman kujera su zo bainar Jam’a su yi baja-kolin manufofin su da muradun su har su kuma ma amsa tambayoyin jama’a.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar wanda ba mamaki zai yi takara a zaben 2019 ya ji dadin wannan abu inda yace hakan zai ba al’umma dama su gane banbanci tsakin zare da abawa a wajen tsayawa takarar zabe.

Kamar yadda Jaridar Punch ta rahoto, Shugaban Hukumar zaben na kasa Farfesa Mahmud Yakubukuma ya nemi masu amfani da kafofin sadarwa na zamani su guji yada labaran karya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel