Dakarun Sojin Najeriya sun yi caraf da wani Dan kunar bakin wake a Adamawa (Hotuna)
Rundunar Sojin kasa dake jibge a jihar Adamawa ta samu nasarar yi caraf da wani matashi dan kunar bakin wake a jihar Adamawa, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.
Rundunar ta samu wannan gagrumar nasara ne a ranar Alhamis 3 ga watan Mayu, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito, inda aka hangi matashin dan kunar bakin wajen dauke da rigar Bom da suke daurawa a jikinsu.
KU KARANTA: Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya hallaka mutane 183, mutane 215 sun jikkata
Idan za’a tuna a ranar Talata 1 ga watan Mayu ne wasu yan kunar bakin wake suka afka cikn wani Masallaci dake layin Gwanjo dake cikin wata kasuwa a garin Mubi na jihar Adamawa.
Wannan mummunan hari ya hallaka sama da mutane ashirin da bakwai, 27, tare da jikkata mutane da dama, Harin ya zo ne a daidai lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo daga kasar Amurka, inda ya tattaunawa da shugaba Trump kan batutuwan da suka shafi matsalolin ta’addanci a Najeriya.
A wani labarin kuma Najeriya ta biya dala miliyan 400 ga gwamnatin kasar Amurka don siyan jiragen yaki na zamani guda 12 a wani mataki na kara kaimi da yakin da rundunar Sojojin Najeriya ke yi da yan ta’adda Boko Haram.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng