Gasar harbi a hukumar soji: Mace ta bawa maza mamaki
Wata mace soja, Cpl. Vivien Ogbuah, dake sansanin hukumar soji na 3 dake Jos ta lashe kofin gasar iya harbi na shekarar nan. Rundunar soji ta 3 dake Rukuba a Jos ne ta shirya gasar.
An kammala gasar ta tsawon kwana hudu da ta kunshi dakarun soji daga sansani daban-daban a yau, Alhamis.
Bayan zama zakara a gasar harbin dakarun soji ta kowa da kowa, Vivien ta lashe gasar harbi ta mata zalla.
DUBA WANNAN: Matan Najeriya sun gindaya wasu sharuda 8 kafin goyan bayan duk wani mai son kuri'ar su a 2019
Da yake jawabi yayin kammala gasar, shugaban rundunar soji a jihar, Manjo Janar Benjamin Ahanotu, da Birgediya janar Aliyu Abdullahi, ya wakilta ya yabawa dakarun sojin bisa halayyar tarbiya da kwarewa da suka nuna yayin gasar.
An shirya gasar ne tsakanin kananun sojoji daga barikin soji dake jihohin Filato da Bauchi.
A wata rahoton da Legit.ng ta kawo muku "Wata lauya ta kashe mijin ta ta hanyar yanke masa al'aura sannan ta saka su cikin hannun sa na dama a rukunin gidajen Diamond dake Sango-Tedo a Legas.
'Yan sanda sun bayyana lamarin da ya faru da misaln karfe 7:30 na safiyar yau, Alhamis, da cewar babu kyan gani.
Marigayin, Otike Odibi, dan asalin jihar Delta, wanda shi ma lauya ne, ya auri matar sa, Udeme Odibi, 'yar asalin jihar Akwa Ibom, shekaru uku da suka wuce.
Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar, Legas SP Chike Oti, ya ce DPO din su dake Ogomah a Ajah aka fara kira tare da sanar da shi cewar matar Mista Otike Odibi ta kashe shi a gidan su dake unguwar Sango-Tedo.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng