Abubuwan da dokar Birtaniyya ta ba Sarauniyar Ingila damar aiwatarwa

Abubuwan da dokar Birtaniyya ta ba Sarauniyar Ingila damar aiwatarwa

Mun kawo maku wasu daga cikin karfin ikon da Sarauniyar Ingila ta ke da shi a kasar ta. A Birtaniya dai har yanzu Sarauniyar ta na da martaba kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada tun tale-tale.

Sai dai yanzu Ministocin kasar ne ke da damar aiwatar da wadannan ayyuka na Sarauniya. Sarauniyar dai tana cikin abin da ya sa tsarin Damukaradiyyar Kasar yake da karfi. Ga dai ire-iren karfin da aka ba Sarauniyar Kasar.

Abubuwan da dokar Birtaniyya ta ba Sarauniyar Ingila damar aiwatarwa
Sarauniyar Ingila tare da Kocin Arsenal a wani tsohon hoto

1. Karfin dakatar da ‘Dan Majalisa

A siyasance dai Sarauniyar Ingila tana da damar korar mutum daga Majalisa idan ya saba doka a Birtaniya.

KU KARANTA

2. Sa hannu a dokokin kasa

Sannan kuma ita Sarauniyar kasar ce ke da ikon sa–hannu a kudirin Majalisa da za a maida doka har yanzu a Ingila.

3. Tsige Ministoci

Bayan dakatar da ‘Yan Majalisu kuma Sarauniyar na iya tsige Minista daga mukamin sa kuma tana da damar nada wani.

4. Cire Firayim Minista

Haka kuma dai Sarauniyar tana da ikon nada Firayim Minista bayan zabe ko kuma idan na-kan-kujera yayi murabus.

5. Shirya yaki

A dokar Ingila Sarauniya ce ta ke da ta cewa wajen jefa kasar zuwa yaki. Yanzu dai Firayim Minista da Majalisa ke aiwatar da wannan.

A doka dai Sarauniyar na iya cewa a fasa yanke wani hukunci da aka zartar ban da ikon da ta ke da shi kan Sojojin kasar. Bayan nan kuma ma dai duk wani fasfon kasar akwai sunan ta a jiki. Haka kuma Sarauniyar Ingila ta fi karfin a tuhume ta a kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng