Hatsarin mota dauke da man fetur a garin Zing yayi sanadiyar rasa rayyuka da dukiyoyi

Hatsarin mota dauke da man fetur a garin Zing yayi sanadiyar rasa rayyuka da dukiyoyi

- Wata mummunan hatsarin motoccin tanka da ya faru a garin Zing yayi sanadiyar mutuwar mutane 8 da raunana wasu

- Hatsarin ya faru ne dalilin matsalar birke da ya janyo tanka mai dauke da man fetur ta fada wa wata motar mai dauke da man fetur kuma gobara ta tashi nan take

- Wutar da ta tashi tayi wuyar kashewa saboda hukumar kashe gobara basu samu zuwa wurin ba

Mun samu rahoton wani mummunar hatsarin motoccin tanka dauke da man fetur da ya faru a garin Zing da ke jihar Taraba inda mutane da yawa suka rasa rayyukansu tare da asarar dukiyoyi masu yawa.

Kamar yadda Voa Hausa ta ruwaito, tankokin man fetur ne guda biyu sukayi karo kuma suka kama da wuta a garin na Zing sakamakon rashin birki wanda hakan yayi sanadiyar salwantar rayyuka da dukiyoyi musamman shaguna da ke bakin titi.

Hatsarin mota dauke da man fetur a garin Zing yayi sanadiyar rasu rayyuka da dukiyoyi
Hatsarin mota dauke da man fetur a garin Zing yayi sanadiyar rasu rayyuka da dukiyoyi

DUBA WANNAN: Majalisar zartarwa ta ware N245bn don gina tituna da wasu muhimman aiki - Fashola

Wani ganau yace mutanen garin sunyi kokarin kashe wutar amma ta fi karfin su kasancewar babu jami'an hukumar kashe gobara a kusa da zasu taimaka musu. Wutar tayi bana sosai saboda ta faru ne yayin da ake cin kasuwar garin na Zing.

Mai magana da yawun Hukumar Yan sandan jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin inda yace mutane takwas sun riga mu gidan gaskiya kuma an garzaya da wasu da dama asibiti inda suke karabar magani.

Mai magana da yawun yan sandan ya kara da cewa birkin tankar da ke dauke da man fetur ne ya tsinke kuma hakan yasa ta buga wata mota da ita ma ke dauke da man fetur din inda dukkansu biyu suka kama da wuta nan take.

Hukumar yan sandan na cigaba da gudanar da bincike don tabbatar da adadin mutanen da suka rasa rayyukansu da kuma wadanda suka sami rauni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164