Masarautar Dutse a jihar Jigawa ta tube rawanin dan tsohon gwamna Sule Lamido
Masarautar Dutse a jihar Jigawa ta amince da tube rawanin dakataccen hakimin garin Bamaina, Mustapha Lamido.
Tube hakimin dake kunshe cikin wata takarda da sakataren masarautar ta Dutse, Amadu Malami ya sakawa hannu.
Tubewar da aka yi masa ta fara aiki nan take kuma bada dadewa ba za a nada sabon hakimin da shugabancin garin Bamaina dake karkashin karamar hukumar Birnin Kudu.
Tube hakimin ya biyo bayan tabbatar da shigar sa cikin lamauran siyasa dumu-dumu.
Tsohon hakimin kuma Santurakin Dustse, Mustapha Lamido, da ne ga tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido. Dukkan su na fuskantar tuhumar almundahana da badakala da kudin mutanen jihar Jigawa lokacin da Lamido ke mulki.
DUBA WANNAN: Siyasar Gado: Jerin wasu 'ya'yan tsofin 'yan siyasa da zasu yi takara a jihar Kano
An gurfanar da su gaban kotu tare da hakimin Kiyawa, Aminu Abubakar.
Sule Lamido na daga cikin masu neman jam'iyyar PDP ta tsayar da su takarar shugaban kasa yayin da dan sa, Mustapha, da aka tube daga mukamin ke takarar kujerar Sanatan jihar Jigawa ta tsakiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng