Yaron Sarkin Saudiyya ya biya naira biliyan 18 sadakin auren budurwarsa mai shekaru 25

Yaron Sarkin Saudiyya ya biya naira biliyan 18 sadakin auren budurwarsa mai shekaru 25

Rahotanni sun tabbatar da wani Yariman kasar Saudiyya, yaron Sarkin Salma, Sultan Bin Salman ya biya zambar kudi dalan Amurka miliyan 50, kimanin naira biliyan 18 kenan a matsayin sadakin auren wata budurwasa mai shekaru 25.

Jaridar Punch ta ruwaito wata ma’abociyar kafar sadarwar zamani na Twitter, Amal Abdul ce ta bayyana wannan labari a shafinta, inda tace Amarya da ba’a bayyana sunanta ba yar asalin kasar hadaddiyar Daular Larabawa, wato Dubai.

KU KARANTA: Da kamar wuya, gurguwa da auren nesa: Wani Gwamnan a Najeriya zai fara biyan ma’aikatan jiharsa kudin bacci

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Amaryar ta samu kayatattun kyautuka da dama daga jama’a da daban daban, da suka hada da yan uwa da abokan arziki.

Yaron Sarkin Saudiyya ya biya naira biliyan 18 sadakin auren budurwarsa mai shekaru 25
Sultan Bin Salman da Amaryarsa

Wannan biki bidiri ya gudana ne a babba Otal din nan na kasar Kuwait mai suna Burj Alshaya, wanda ya smau halartar Angon da abokansa suka shigo manyan motocin alfarma kirar Range Rover guda Talatin, 30.

Bugu da kari Ango Sultan ya bawa sahibarsa akwatunan kaya guda Talatin, 30, haka zalika ya baiwa matar kyautan wani Keken doki cike da kayayyakin kyale kyale da suka hada da gwalagwalai da lu’lu da sauransu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng