Karin albashi: Bani gishiri in baka manda zamu yi da yan siyasa a zaben 2019 – Kungiyar kwadago

Karin albashi: Bani gishiri in baka manda zamu yi da yan siyasa a zaben 2019 – Kungiyar kwadago

Kungiyar kwadago ta ma’aikatan Najeriya ta dauki alwashin yin amfani da kuri’un yayanta wajen karya duk gwamnatin da ta gagari biyan karancin albashi da a yanzu haka ake gab da cimma tabbatar da shi, kamar yadda Premium Time ta ruwaito.

Shugaban kungiyar kwadago,NLC, Ayuba Wabba ne ya yi wannan barazana a ranar Talata, 1 ga watan Mayu a yayin bikin ranar ma’aikata daya gudana a garin Abuja, inda yace: “A shirye muke mu yaki duk wata gwamnati da kuma ma’aikatu masu zaman kansu da suka gaza biya karancin albashin da muke fafutuka akansa.

KU KARANTA: Innalillahi wa inna ilaihi rajiun: An samu tashin bama bamai a garin Mubi

“Muna da karfin kuri’a, zamu tabbatar da karya da duk wata gwamnati da ta gaza biyan sabon albashi, ta hanyat hana su kuri’in ma’aikata, yan fansho da iyalansu gaba daya.” Haka zalika yayi kira ga ma’aikata da kada su lamunci duk wani yunkuri na rage karancin albashin.

Karin albashi: Bani gishiri in baka manda zamu yi da yan siyasa a zaben 2019 – Kungiyar kwadago
Kungiyar kwadago

Bugu da kari Wabba yayi kira ga shugaban kasa da kada ya aika ma duk jihar da ta gagara biyan karancin albashi kudin mai da ake basu a kowanne wata, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

A nasa jawabin, Kaakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya yi alkawarin zasu kammala aiki ka kudurin tabbatar da karancin albashi cikin kankanin lokaci matukar bangaren zartarwa ta aiko musu da kudurin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng