Kasashen yamma sun sako kasar Iran a gaba

Kasashen yamma sun sako kasar Iran a gaba

- Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya tattauna da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho, inda suka jima suna magana akan kasar Iran

Kasashen yamma sun sako kasar Iran a gaba
Kasashen yamma sun sako kasar Iran a gaba

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya tattauna da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ta wayar tarho, inda suka jima suna magana akan kasar Iran.

DUBA WANNAN: Trump ya nemi goyon bayan Najeriya don basu bakuncin gasar cin kofin duniya na 2026

A bayanin da fadar gwamnatin Kremlin ta kasar Rasha ta fitar ta sanar da cewa, shugabannin biyu sunyi nazari tare da duba batun da hukumar leken asiri ta kasar Isra'ila tayi na cewa, har yanzu kasar Iran tana sarrafa makamin nukiliya.

A yayin tattaunawar tasu kasar Rasha ta sake dauko maganar yadda take wani bangare na yarjejeniyar da aka yi da ita, da kuma yadda ta dauki yarjejeniyar da muhimmanci.

A karshen wayar tasu Putin na kasar Rasha da kuma Netanyahu na kasar Isra'ila sun tattauna aka halin da ake ciki a kasar Siriya dama yankin gabas ta tsakiya baki daya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng