Gwamnati ta haramta sarrafa maganin tari mai sinadarin kodin

Gwamnati ta haramta sarrafa maganin tari mai sinadarin kodin

- Daga karshe, gwamnatin tarayya ta haramta shigo da maganin tari mai dauke da kodin

- An dauki wannan matakin ne saboda yadda mutane suke shan maganin ba bisa ka'ida ba don ya sa su maye

- Ministan yace za'a maye gurbin sinadarin na codeine da dextromethorphan wanda bai kai shi karfi ba

Ma'aikatan lafiya ta kasa ta bawa Hukumar kula da abinci da magunguna na kasa NAFDAC umarni a kan hana shigo da duk wani maganin tari mai dauke da Kodin da ke sanya maye.

Ministan lafiya Farfesa Isaac Adewale ya bayyana haka a ranar Talata 1 ga watan Mayu a ofishinsa dake Abuja.

Gwamnati ta haramta sarrafa maganin tari mai sinadarin kodin
Gwamnati ta haramta sarrafa maganin tari mai sinadarin kodin

Yace hakan ya zama dole duba da yanda ake fama da masu sham Kodin a kasar, mussaman a arewacin Najeriya, yace a maimakon amfani da kodin din za'a musanya shi da Dextromethorpan a cikin maganin saboda baikai kodin karfi ba.

Sannan ya bawa NAFDAC da Kungiyar masana kimiyyan magunguna (PCN) umarnin sanya ido da kuma sanya kafar wando daya wajen hana siyar da duk wani maganin tari da yake dauke da Kodin a cikin sa face anga shaidar rubutu.

Yace NAFDAC sunyi ganawa ta gaggawa da Kungiyar masu sarrafa magunguna (PMGMAN) don sanar dasu akwai takunkumi akan sabbin aikace aikace da sabunta yin rigista akan maganin tarin dake dauke da kodin..

PCN ta bada umarnin a cigaba da tilastawa masu saida magungu na da marasa lafiya da duk wasu masu saida magani wajen bin wannan doka a kasar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164