Sanata Shehu Sani ya mika kan sa ga hukumar 'yan sanda bisa zargin kisa
Sanata mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya amsa gayyatar da hukumar 'yan sanda tayi masa bisa zargin hannun sa a cikin wani laifin kisa.
Hukumar ta 'yan sanda ta gayyaci Sanatan ne biyo bayan ambaton sunan sa da wani da take tuhuma da laifin kisan kai ya yi yayin gudanar da bincike.
Shehu Sani, a shafin sa na Tuwita, ya bayyana cewar ya amsa gayyatar 'yan sanda da safiyar jiya, Litinin, a babban ofishin hukumar na jihar Kaduna.
Sanatan ya ce ya isa ofishin hukumar da misalin karfe 10:45 na safe. Sannan ya kara da cewar bayan ya rubuta bayanin sa dangane da zargin da ake yi masa, an bar shi ya tafi bisa dogaro da matsayin sa.
A kwanakin baya ne kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna, Mista Austin Iwar, ya aike da wasikar gayyata ga Sanata Shehu Sani tare da bukatar ya bayyana a hukumar ranar 30 ga watan Afrilu domin bayar da jawabi a wani laifin kisa da sunan sa ya fito.
DUBA WANNAN: Hukumar 'yan sanda ta dakume wani dan takarar gwamna a jihar Adamawa, ta bayar da dalili
Wani mutum, Isa Garba, da ake zargi da aikata kisan wani mutum, Lawal Madagu, ya ambaci sunan Sanata Shehu Sani a wurin jami'an 'yan sanda yayin tuhumar sa. Daga baya dai ya bayyana cewar ya ambaci sunan Sanatan ne saboda tsananin.
Kwamishinan 'yan sanda a jihar ya musanta cewar binciken Sanatan yana da alaka da siyasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng