Kasar Saudiyya ta zartar hukuncin kisa kan matashin da ya yi ridda tare da yin batanci ga Annabi
Kasar Saudiyya ta zartar da hukuncin kisa a kan wani mutum da ya yi ridda tare da yin kalaman batanci ga Annabi.
Hankalin hukuma ya kai kan Ahmad Al-Shamri a shekarar 2014 bayan ya saka wasu faifan bidiyo dake nuna akidar mulhidanci a dandalin sada zumunta. An gurfanar da shi gaban kotu bisa tuhumar sa da batanci da kuma mulhidanci tare da yanke masa hukuncin kisa a shekarar 2015.
Da farko matashin, Al-Shamri; mai shekaru 20, ya bayyana cewar yana cikin maye ne lokacin da ya aikata laifin da ake tuhumar sa da shi saidai uzurin shi bai samu shiga ba a gaban kotun.
Hukumomi a kasar Saudiyya sun yi dogaro da ayoyin Qur'ani wajen yanke wa Al-Shamri hukunci. Za kashe shi ta hanyar harbi ko datse masa kai.
DUBA WANNAN: Da dumin sa: Abubuwa biyar da Trump ya fada a kan Najeriya yayin ganawa da Buhari
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty ta saka kasar Saudiyya a matsayin kasa ta uku a jerin kasashe dake zartar da hukuncin kisa a kan mutane.
Ra'ayin masu amfani da dandalin sada zumunta ya rabu a kan wannan hukunci da aka zartar a kan Al-Shamri, inda wasu ke nuna cewar hukuncin ya yi tsauri yayin da wasu kuma ke murna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng