Shugaban Amurka Trump ya koka da kashe Kiristoci a Najeriya (Bidiyo)

Shugaban Amurka Trump ya koka da kashe Kiristoci a Najeriya (Bidiyo)

- Donald Trump yayi tir da yadda ake zubar da jinin Kiristoci a Najeriya

- Shugaban na Amurka yace ba fa za su zura idanu a cigaba da wannan ba

- Donald Trump ya gana da Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari

Dazu nan ne Shugaban kasar Najeriya watau Muhammadu Buhari ya gana da Shugaba Donald Trump. Shugaba Buhari ya gana da takwaran na sa ne a fadar Shugaban kasar Amurka na White House da ke babban Birnin Washington DC.

Shugaban Amurka Trump ya koka da kashe Kiristoci a Najeriya (Bidiyo)
Shugaban Amurka Trump lokacin da ya gana da Buhari

Shugaban na Amurka Donald Trump yayi tir da yadda aka kashe Kiristoci a Najeriya. Kashe-kashen na faruwa ne a Arewacin Kasar a Jihohi irin su Benuwe da Taraba da kuma Adamawa har da Kudancin Jihar Kaduna tun kwanaki.

KU KARANTA: Duniya ta kosa ta ji yadda ganawar Buhari da Trump za ta kasance

Donald Trump yace za a kawo karshen wannan mummunan abu lokacin da ya gana da Shugaba Buhari. Shugaban na Kasar Amurka Mista Trump ya nuna cewa sam ba za su bari a cigaba da kashe Kiristoci a Najeriya ba su na kallo da idanun su.

Idan ku na biye da mu dai kun ji tun a baya cewa dama tattaunawar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Donald Trump za ta fi karfi ne a kan sha’nin tsaro da tattalin arziki da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Kusan dai wannan ne karon farko da Shugaban kasar Bakar Afrika ya gana da Shugaban na Amurka Donald tun da yau mulki. Shugaba Buhari ya kuma yabawa kokarin da kasar Amurka take yi wajen yaki da ta’addanci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: