Kasafin kudin 2018: Tsagerun yankin Naija-Delta sun yi barazana ga gwamnatin tarayya

Kasafin kudin 2018: Tsagerun yankin Naija-Delta sun yi barazana ga gwamnatin tarayya

Wasu kungiyoyin tsagerun yankin Naija-Delta karkashin wata hadaddiyar kungiya mai suna Urhobo Liberation Force tayi barazana ga gwamnatin tarayya.

Kungiyar ta ce zata koma aikin lalata matatu da bututun danyen man fetur matukar gwamnati bata ware isassun kudi ga jami'ar albarkatun man fetur ta FUPRE dake jihar Delta ba.

Kungiyar ta yi wannan barazana ne ta hannun kwamandojin ta na tsaro da shirye-shirye, Janar Orubu Ekpe da Mike Agbalele.

Kasafin kudin 2018: Tsagerun yankin Naija-Delta sun yi barazana ga gwamnatin tarayya
Tsagerun yankin Naija-Delta

Kungiyar ta ce ta bawa gwamnatin tarayya wa'adin kwana 14 ta duba bukatar su.

Tsagerun sun ce an ware kabilar su ta Urhobo duk da kasancewar ta kabila ta biyar mafi yawan jama'a a Najeriya kuma ga arzikin man fetur.

DUBA WANNAN: Tsaurin ido: Wata budurwa ta shararawa dan sanda mari, idon ta ya raina fata

A cewar kungiyar, shugaba Buhari ya ki ya bawa 'yan kabilar gurbin ministan jihar Delta.

An samu lafawar tashe-tashen hankula sakamakon aiyukan tsagerun yankin Naija-Delta.

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Marigayi Umar Musa 'Yar'adua, ne ya fara kirkiro shirin yin afuwa ga tsagerun yankin Naija-Delta bayan hawan sa mulki a shekarar 2007.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng