Siyasar Gado: Jerin wasu 'ya'yan tsofin 'yan siyasa da zasu yi takara a jihar Kano

Siyasar Gado: Jerin wasu 'ya'yan tsofin 'yan siyasa da zasu yi takara a jihar Kano

Karatowar kakar zaben bai-daya na shekarar 2019, wasu daga tsoffin yan siyasar kasar nan da suka jima suna jagorantar al'umma a mataki daban-daban, na wani yunkuri na fito da 'ya yansu a gwabza da su a kakar zabe mai zuwa.

A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar jiya Lahadi, ya bayyana wasu 'yan siyasa daga jam'iya mai mulki APC da kuma babbar jam'iyyar adawa ta PDP na ta kokarin an dama da 'ya 'yansu su a kakar zabe mai zuwa.

'Yan siyasar dake wannan yunkurin dora 'ya 'yansu sun hada da:

Tsohon gwamna Kano kuma sanata mai wakiltar Kano ta kudu a zauren majalisar dattijai, Ibrahim Kabiru Gaya, ministan cikin gida, janaral Abdulrahman Bello Dambazau mai ritays, Ambasada Aminu Wali, Alhaji Farouk Iya, Alhaji Nasiru Aliko Koki da kuma Alhaji Bashir Ibrahim Gwammaja.

Siyasar Gado: Jerin wasu 'ya'yan tsofin 'yan siyasa da zasu yi takara a jihar Kano
Wasu tsofin 'yan siyasa a jihar Kano

Daily Trust ta rawaito cewa, dan gidan Aminu Wali, Sadiq Aminu Wali, zai fito neman takarar kujerar gwamnan Kano, yayin da Alhaji Anas dan gidan Ibrahim Kabiru Gaya na shirye-shiryen neman kujerar majalisar wakilai ta tarayya dake wakiltar Gaya/Ajingi/Albasu.

Alhaji Aminu Bashir Ibrahim Gwammaja kuma zai nemi kujarar wakilai ta tarayya dake wakiltar Tarauni karkashin jam'iyyar APC, yayin da Alhaji Hamza dan gidan Alhaji Farouk Iya ke son neman kujerar wakilai dake wakiltar karamar hukumar Tarauni a karkashin jam'iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Cikin Hotuna: Dangote da wasu jiga-jigan 'yan Najeriya sun ziyarci Buhari a Amurka

Shi kuwa Alhaji Bashir Nasiru Aliko Koki da Alhaji Shamsuddeen Abdulrahman Bello Dambazau za su kara neman kujerar wakiltar Takai/Sumaila da kuma Dala a majalisar wakilai ta tarayya karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Shugaban jam'iyyar PDP na jahar Kano, sanata Mas'ud El-Jibril Doguwa, ya tabbatar da cewa, uwar jam'iyya ta jaha na sane da cewa Alhaji Hamza Faruk Iya da kuma Alhaji Sadiq Aminu Wali na da bukatar tsayawa takara karkashin jam'iyyar su. Ya kara da cewa Alhaji Hamza Faruk Iya tuni ya sanar da shugabancin jam'iyyar ma.

Wani jigo a jam'iyyar APC da ya roki a sakaye sunansa ya ce, wannan tsari ba lallai ya haifarwa tsarin demokrasiyya da mai ido ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng