Yanzu-Yanzu: Sojin Saman Najeriya sunyi ragaraga da sansanin yan Boko Haram da ke Tumbum Gini

Yanzu-Yanzu: Sojin Saman Najeriya sunyi ragaraga da sansanin yan Boko Haram da ke Tumbum Gini

Hukumar sojin saman Najeriya ta ce dakurun rundunar Lafiya Dole sunyi nasarar ragargaza wani sansanin shirye-shirye na kungiyar Boko Haram da ke garin Tumbum Gini wanda ke yammacin garin Borno.

Kakakin sojin saman Najeriya, AVM Olatokunbo Adesanya ne ya tabbatar da hakan a yau Asabar a wata sanarwa da ya fitar a garin Abuja inda yace an kai samamen ne a ranar 27 ga watan Afrilu.

Yace wani jirgin sojin saman na musamman ne ya fara gudanar da shawagi inda yayi nazarin matsugunin yan ta'adan tare da nazarin irin lahanin da harin zai haifar.

KU KARANTA: Dalilin da yasa gwamnoni basu iya samar da ingantaccen tsaro a jihohinsu - Yari

Hotunan da jirgin kirar Alpha Jet ya bayyana ya nuna cewa luguden wutar da akayi wa sansanin na yan Boko Haram din ya lalata dukkan motoci da ababen hawa tare da wasu kayaykin su, wanda hakan ya kara karya lagwan yan kungiyar.

Bugu da kari, a karshen harin, dukkan sansanin ya kama da wuta kuma ya kone kurmus wanda hakan ya nuna cewa an murkushe sansanin da duk wanda suke ciki baki daya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel