An kashe Hausawa da yawa a jihar Benuwe

An kashe Hausawa da yawa a jihar Benuwe

- Sarkin Hausawa na garin Makurdi, Alhaji Bello Sallau Abdulrahman, yace an kashe mutane 8, sama da mutum 20 sunji rauni, sannan kuma an nemi mutum 11 ba a gansu ba, yayinda aka kone shaguna masu dunbin yawa a yankin, a lokacin da matasan kabilar Tiv suka kai musu hari

An kashe Hausawa da yawa a jihar Benuwe
An kashe Hausawa da yawa a jihar Benuwe

An kashe mutane da yawa hare-haren da aka kai yankin Hausawa a garin Makurdi, babban birnin jihar Benuwe, kamar yanda shugabannin yankin suka bayyana.

Sarkin Hausawa na garin Makurdi, Alhaji Bello Sallau Abdulrahman, yace an kashe mutane 8, sama da mutum 20 sunji rauni, sannan kuma an nemi mutum 11 ba a gansu ba, yayinda aka kone shaguna masu dunbin yawa a yankin, a lokacin da matasan kabilar Tiv suka kai musu hari.

DUBA WANNAN: Buhari ya tsallake rijiya da baya, yayinda wasu Sanatoci suka yi yunkurin tsige shi

A lokacin da yake zantawa da manema labarai, yace; "A ranar Talata, mun ga mutanen mu suna gudu cikin tashin hankali a cikin gari, a lokacin da aka kashe malaman coci biyu a kauyen Dukwayango, ba a jima da wannan ba sai ganin matasan kabilar Tiv muka yi suna kawo mana hari, a yanzu haka da nake magana dauk sun kashe mutane sama da 8, sunji wa mutane sama da 20 ciwo, mun kuma nemi mutane 11 mun rasa, bayan haka kuma sun kone mana shaguna masu tarin yawa."

Sarkin yace al'ummar Hausawa suna zaune cikin tsoro a yankin. Ya ce, yayi mamakin dalilin da yasa aka kawo wa Hausawa hari, saboda su ba makiyaya bane, ba kiwo suke yi ba, mai yasa za ake zargin su da kai hari a wasu yankuna na jihar.

"Mu ba makiyaya bane, ba kiwo muke yi ba , mu kasuwanci ne ya kawo mu, wannan hare-haren yana faruwa ne a kauyuka da kuma cikin daji, dalilin mene yasa Tiv suke kashe mana mutane," inji shi.

Sarkin yace ya gargadi mutanen shi akan kada su sake su dauki doka a hannun su, sannan kuma ya bukaci gwamnatin tarayya data kawo musu dauki, kafin matsalar ta mamaye wasu yankunan na jihar.

Babban limanin Izala na garin Makurdi, Sheikh Shu'aibu, ya bayyana wa manema labarai cewar shi da idon shi yaga gawarwaki na mutum 27 a babban asibitin Makurdi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng