Duba irin tarba da shugaba Buhari ya samu daga mutanen jihar Bauchi
Mutanen jihar Bauchi sun yi fitar dangon fari domin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin da ya isa jihar a wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu.
Wannan shine karo na farko da Buhari ya ziyarci jihar Bauchi tun bayan hawan sa karagar mulki a shekarar 2015.
Tun bayan shigowar sa siyasa a shekarar 2003, Buhari, na da matukar farin jini a wurin mutanen jihar Bauchi.
A baya an taba saka ranar da Buhari zai kai ziyara jihar Bauchi amma kuma hakan bata yiwu ba saboda wasu dalilai.
DUBA WANNAN: Ana wata ga wata: Gwamnatin jihar Kaduna ta maka El-Zakzaky a kotu bisa wasu caji takwas
A yayin ziyarar sa ta yau, shugaba Buhari zai kaddamar da wasu aiyuka da gwamnatin jihar ta yiwa jama'ar ta tare da jagorantar rabon kayan noma ga manoma da jihar ta samar.
Daga cikin kayayyakin da shugab zai raba ga manoma akwai motocin noma (Tractor) 500, motocin daukan amfanin gona masu taya uku, babura da buhunhunan taki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng