Zargin badakalar: Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa ya amsa laifin sa
Babban darektan hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA), Injiniya Mustapha Maihaja, ya shaidawa kwamitin bincike na majalisar wakilai cewar ya yi kuskure.
Kwamitin na binciken hukumar ta NEMA da sabawa ka'ida wajen rabon kayan agaji da kuma bayar da wasu kwangiloli da hukumar ta yi a wasu jihohin arewa maso gabashin Najeriya.
Binciken kwamitin ya fi mayar da hankali ne a kan rabon or kin raba kayan agaji da kuma badakalar wasu kudi har biliyan N8bn a jihohi biyar: Borno, Yobe, Gombe, Adamawa da Bauchi.
Wakilan gwamnatocin jihohin Yobe, Gombe, Bauchi da Taraba da suka bayyana a gaban kwamitin sun tabbatar da cewar hukumar NEMA bata sanar da su ba kafin raba kayan agaji a jihohin kamar yadda doka ta tanada ba.
DUBA WANNAN: Wasikar Buhari ta jawo barkewar cece-kuce da rabuwar kayuwa a tsakanin 'yan majalisar wakilai
Da yake amsa tambayar kwamitin, Injiniya Mustapha, ya bayyana cewar duk da cewar abinda hukumar tayi kuskure ne, sun yi hakan ne saboda bukatar gaggauta rabon kayan agajin ga mabukata tare da bayar da kwangilar sayen wasu karin kayayyakin. Kazalika ya shaidawa cewar, a jihar Yobe sun tuntubi gwamnatin jihar kuma har ta aiko da wasikar amincewa da rabon kayan agaji a jihar.
Kwamitin ya bukaci duk kamfanoni da aka bawa kwangila da ma'aikatar kasafi da ta Noma da duk masu hannu cikin badakalar kwangila a hukumar NEMA su bayyana a gaban ta tare da bukatar shugaban hukumar, Injiniya Mustapha, ya zo da dukkan takardun bayar da kwangilolin a zama na gaba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng