Bayan ganawar sirri da Buhari, Alkalin alkalan Najeriya ya ce alkalai basu da laifi

Bayan ganawar sirri da Buhari, Alkalin alkalan Najeriya ya ce alkalai basu da laifi

Alkalin alkalan Najeriya, Jastis Walter Onneghen, ya bayyana cewar tafiyar hawainiya da shari'a keyi a kasar nan ba laifin alkalai bane.

Onneghen na wannan furuci ne a fadar gwamnatin tarayya bayan wata ganawar sirri da ya yi da shugaba Buhari a yau, Talata.

Onneghen ya ce babu wani alkali da zai gama sauraron kara kuma ya ki yanke hukunci tare da bayyana yawan daga sauraron kara a matsayin abinda ke kawo cikas a ga batun yanke hukunci.

Bayan ganawar sirri da Buhari, Alkalin alkalan Najeriya ya ce alkalai basu da laifi
Ganawar Buhari da Alkalin alkalan Najeriya Onnoghen

Sannan ya kara da cewar masu shigar da kara ne ke neman a daga karar domin su samu damar tattara ko gabatar da shaidu, ita kuma kotu take basu dama, a saboda haka bai kamata a ga hakan a matsayin laifin alkali ba.

DUBA WANNAN: Yanzu:yanzu: Dino Melaye ya kubuce daga hannun ‘yan sanda, wasu tsageru ne suka kwace shi

Da yake bayyana dalilin ziyarar sa ga shugaba Buhari, Onneghen, ya ce ya je yiwa shugaban kasar ban gajiya ne bayan dawowar sa daga kasar Ingila inda ya halarci taron kasashen common wealth.

Onnoghen ya ce ya yaba da kokarin alkalan Najeriya tare da bayyana cewar suna iya matukar kokarin su kuma yana alfahari da su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel