Iyalan wani ‘Dan Majalisa sun mutu a wani mummunan hadarin mota

Iyalan wani ‘Dan Majalisa sun mutu a wani mummunan hadarin mota

- Wani ‘Dan Majalisa a Zamfara ya rasa ‘Ya ‘yan sa da ‘Yanuwan sa a hadari

- Motar da ta dauko Iyalin ‘Dan Majalisar dai tayi hadari ne a hanyar Sokoto

- Mutane 10 su ka rasu nan take yayin da sauran 2 ke kwance a asibiti yanzu

Mun samu labari cewa wani ‘Dan Majalisar Dokoki na Jihar Zamfara Honarabul Saidu Yarkufoji ya gamu da jarrabawar ubangiji bayan da ‘ya yan cikin sa 3 su ka wuce lahira a dalilin wani hadarin mota a ranar Lahadin nan da ta wuce.

Iyalan wani ‘Dan Majalisa sun mutu a wani mummunan hadarin mota
Wani 'Dan Majalisa ya rasa iyalan sa a hadarin mota

Iyalan wannnan ‘Dan Majalisa sun mutu ne a wani mugun hadarin mota kamar yadda Hukumar FRSC da ke kula da hanyoyin kasar ta bayyan a jiya Litinin. Bayan yaran ‘Yan Majalisar da su ka rasu akwai kuma wasu jikokin sa 4.

Har wa yau Hukumar dillaci na manema labarai watau NAN ta tabbatar da cewa ‘Dan Majalisar ya kuma rasa wasu ‘Yan uwan sa mata 2 da Direban motar a kan hanyar Sokoto zuwa Gusau. Wannan hadari ya auku ne a Ranar Lahadi.

KU KARANTA: Kwankwaso ya sha yabo daga bakin Gwamna Ganduje

Wata katuwar motace dai kirar Volkswagen mai daukar fasinjoji 12 tayi artabu da gingimarin kamfanin Coco-cola inda mutane 10 su ka wuce lahira. Kusan duka mutanen da ke cikin mota mata ne. Sauran 2 dai su na asibiti yanzu.

Ku na da labari cewa Sanata Dino Melaye dai ya fadawa BBC cewa ana neman ganin bayan sa a Najeriya saboda fadan gaskiyar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng