Wasu tsageru a jihar Ribas sun takali sojoji, an yi barin wuta da asarar rayuka
Mutane hudu aka tabbatar da an harbe har lahira yayin da wasu da dama suka jikkata a wata arangama tsakanin wasu tsagerun samari masunta a karamar hukumar Bonny dake jahar Ribas da dakarun sojin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewar rikicin ya barke ne yayin da wasu tsagerun samarin yankin suka yi yunkurin farwa sojojin hadin gwuiwa l(JTF) da aka tura yankin don aiwatar da sintiri. Majiyar mu ta tabbatar da cewa, nan take sojojin suka harbe mutum hudu wasu da dama kuma suka raunata.
Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Ribas, Nnamdi Omoni, ya tabbatar da faruwar al'amarin inda ya ce:
"Yanzu haka da muke magana da ku, zan iya tabbatar da mutuwar mutum biyu. Lamarin ya biyo bayan arangama tsakanin sojojin hadin gwuiwa (JTF) da kuma wasu samari daga Finima. An sami musayar wuta tsakanin su amma komai ya lafa." In ji mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Ribas.
A wani labarin mai alaka da wannan, rundunar hukumar soji ta 72 tayi nasarar dawo da zaman lafiya a Otukpo dake jihar Benuwe bayan barkewar wata jimurda bayan wasu 'yan bindiga sun kutsa kai cikin wani wurin taron siyasa inda suka bude wuta.
DUBA WANNAN: Kallon fim din batsa ya saka shi yiwa mahaifiyar sa fyade
A yayin da 'ya'yan jam'iyyar APC ke tsaka da gudanar da taro ne a wani Otal dake kan titin Otukpo, wasu 'yan bindiga suka kutsa kai suka bude masu wuta tare da kashe mutane biyu tare da jikkata wani mutum guda.
Jami'an soji sun mamaye yankin da abin ya faru domin hana barkewar karin wani rikicin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng