Gwamnatin Najeriya ta gardanta maganar da Sarki Sanusi yayi cewa gwamnatin taki amsa goron gayyatar da kasar Amurka ta turo mata

Gwamnatin Najeriya ta gardanta maganar da Sarki Sanusi yayi cewa gwamnatin taki amsa goron gayyatar da kasar Amurka ta turo mata

- Gwamnatin tarayya ta gardanta ikirarin da Sarki Muhammadu Sanusi II yayi na cewa an gayyaci Ministocin Najeriya zuwa wurin taron masu zuba hannun jari a Washington DC

- Sanusi II ya bayyana cewa baza’a amince da irin wadannan halaiyya ba da Ministocin Najeriya da Gwamnoni suke nunawa ba game da wannan gayyatar wadda dama ce ta jawo mutane masu zuba hannun jari a gida Najeriya

- Taron an masa take cewa Najeriya a bude take ga masu bukatar kasuwanci, wanda zai kawo mutane daban daban wuri daya wadanda zasuyi kasuwanci wasu kuma su zuba hannun jari wasu kuma bayar da shawarwari game da harkokin kasuwanci

Gwamnatin tarayya ta gardanta ikirarin da Sarki Muhammadu Sanusi II yayi na cewa an gayyaci Ministocin Najeriya, zuwa wurin taron masu zuba hannun jari a Washington DC, dake kasar Amruka, a ranar 19 ga watan Afirilu shekara ta 2018, amma suka ki halartar taron.

Sanusi II ya bayyana cewa baza’a amince da irin wadannan halaiyya ba da Ministocin Najeriya da Gwamnoni suke nunawa ba game da wannan gayyatar wadda dama ce ta jawo mutane masu zuba hannun jari a gida Najeriya don cgaban kasar.

Gwamnatin Najeriya ta gardanta maganar da Sarki Sanusi yayi cewa gwamnatin taki amsa goron gayyatar da kasar Amurka ta turo mata
Gwamnatin Najeriya ta gardanta maganar da Sarki Sanusi yayi cewa gwamnatin taki amsa goron gayyatar da kasar Amurka ta turo mata

Taron an masa take cewa Najeriya a bude take ga masu bukatar kasuwanci, wanda zai kawo mutane daban daban wuri daya wadanda zasuyi kasuwanci wasu kuma su zuba hannun jari wasu kuma bayar da shawarwari game da harkokin kasuwanci, wanda aka gudanar a Najeriyan House dake kasar Washington.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kama Sanata Melaye a filin jirgin sama

Ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed a ranar Litinin ya bayyan cewa Ministocin da ake maganar cewa sunki halartar taron ba’a gayyacesu bane kuma basa garin Washington DC a lokacin, saboda haka duk wasu maganganu da akeyi game da Ministocin sun karbi katin gayyata amma sunki halartar taron bashi da asali.

A halin da ake ciki shugaban kasa Muhammadu Buhari na cigaba da shan caccaka daga yan Najeriya sakamakon furuci da yayi akan matasan Najeriya a kasar Ingila.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel