Hukumar EFCC zata koma sabon ofishin ta da aka gina a kan biliyan N24bn

Hukumar EFCC zata koma sabon ofishin ta da aka gina a kan biliyan N24bn

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) zata koma sabon ofishin ta da aka kashe biliyan N24bn wajen gina shi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai kaddamar da sabon ofishin da za a bude cikin sati mai zuwa.

Mai rikon kwaryar shugabancin hukumar, Ibrahim Magu, ya bayyana jin dadin sa bisa kammala aikin ginin sabuwar shelkwatar hukumar.

"Ina godiya ga shugaban kasa da ya bawa wannan aiki fifiko. Hakan ya kara jadda aniyar da yake da ita ta yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya. Wannan gagarumin aiki ne da zai saka Najeriya alfahari da shi.

Hukumar EFCC zata koma sabon ofishin ta da aka gina a kan biliyan N24bn
Shugaban Hukumar EFCC; Ibrahim Magu

"Babu wani shugaba a Afrika da ya nuna zallar kishi a bangaren yaki da cin hanci kamar shugaba Buhari. Muna godiya ga ma'aikatu da hukumomin gwamnati bisa goyon baya da gudunmawar da suka bamu wajen ganin aikin sabon ofishin mu ya kammala," inji Magu.

Kazalika Magu ya mika godiya da jinjina ga majalisun Najeriya bisa damuwar da suka nuna game da ginawa hukumar sabon matsuguni.

DUBA WANNAN: Gwamnatin tarayya ta bayyana yadda zata kashe miliyan $322.5 kudin Abacha da ta karbo

Magu ya kara da cewa, hakan ya tabbatar da cewar hukumomin Najeriya zasu iya hada kai da juna domin yaki da cin hanci.

Ana saka ran mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, zai duba sabuwar shelkwatar kowanne lokaci daga yanzu.

An fara gina ofishin ne a karkashin tsohuwar shugabar hukumar EFCC, Farida Waziri.

An fara ware biliyan N18bn domin ginin a shekarar 2010. Ginin na da bene hawa 10.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel