Maganin sanyi, rage kiba da sauran irin amfanin da goro yake yi ga mutum

Maganin sanyi, rage kiba da sauran irin amfanin da goro yake yi ga mutum

Wannan karo mun shiga harkar kiwon lafiya ne inda mu ka kawo maku wasu manyan amfanin goro a jikin ‘Dan Adam kamar yadda binciken masana ya nuna. Ana yawan samun goro ne a kasashe musamman na Afrika irin na mu.

Maganin sanyi, rage kiba da sauran irin amfanin da goro yake yi ga mutum
Goro na maganin sanyi kuma yana rage kiba

Goro na dauke da sinadarin caffeine wanda ya gyara shi sai dai kuma idan caffeine yayi yawa yana iya jawo illa a jikin mutum. Ga dai amfanin goro nan ko da yake yana da ‘daci a baki:

1. A dalilin caffeine din da ke cikin goro, goro na taimakawa wajen ganin abincin da mutum ya ci yayi masa aiki kwarai sannan kuma ya taimaka wajen ganin ya gina jiki.

2. Haka kuma gora na taimakawa wajen zagayawar jini a jikin mutum. Idan mutum na cin goro da kyau, jinin jikin sa zai rika yawatawa a ko ina domin karin lafiya.

KU KARANTA: An saki Sanatan Najeriya da aka kama a filin jirgi

3. Goro na taimakawa kuma wajen markada abincin da mutum ya ci inji masana. Har wa yau Goro kuma na maganin gyatsa da shakuwa da kumburin ciki ko yunkurin amai da tashin zuciya.

4. Goro ya kan taimakawa wajen zaburar da garkuwar jiki. Ganyen goro na maganin wasu cututtuka musamman na sanyi da tari.

5. Jama’a da dama ba su san cewa goro yana maganin cutar kansa musamman wanda ke kama gaban namiji. Goro na taimakawa bangaren da ke taimakawa wajen fitar da ruwan namiji.

Sai dai masu cutar zuciya sai sun bi a hankali domin yawan cin goron na iya yi masu illa. Masana sun ce goro na taimakawa masu nauyin da ke so su rage kiba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel